BBC News, Hausa - Labaran Duniya
Babban Labari
Rayuwar Bayahude ɗaya ta kai ta Falasɗinawa miliyan 10 - Lauyan Isra'ila
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Asabar 01 ga watan Agustan 2026
Me ya sa muryar mace ta sha bamban da ta namiji?
Muryar ɗan Adam wata aba ce ta musamman ƙwarai. Tana isar da sako kan halin da mutun ke ciki ,tana kuma nuna iko , kuma tana ɗauke da ainihin mutumtakarmu.
Yadda gwamnatin Najeriya za ta cire tallafin wutar lantarki a 2027
"Babu wata manufa ta wannan gwamnati ta ƙara kuɗin wutar lantarki fiye da yadda yake a yanzu, idan an cire tallafin," in ji ministan makamashi, Joseph Tegbe.
Abubuwan da suka kamata budurwa ta sani kafin aure
"Babu wani shiri da zai sa mutum ya san duk abin da zai faru a gidan aure. Amma sanin kai, tattauna muhimman batutuwa, lura da halayen wanda za a aura da kyakkyawar fahimta da kuma neman shawara na iya taimaka wa budurwa ta shiga wannan sabon mataki na rayuwa."
BBC ta gano sabbin ɓarnar da Iran ta yi wa sansanonin Amurka da muhimman wurare a yankin Gulf
Sashen BBC Verify mai bincike ya tattara shaidu da ke nuna ɓarna a aƙalla sansanonin soja da muhimman cibiyoyi guda tara a Kuwait, Bahrain, Iraki da Jordan tun bayan fara sabon rikicin da ya ɓarke a ranar 12 ga Yulin 2026.
Arsenal ta miƙa tayin Guimaraes, Inter ta haƙura da Romero
Arsenal da Newcastle sun amince da farashin Bruno Guimaraes, Inter Milan ta ƙara kuɗin da ta taya Curtis Jones yayin da Cristian Romero na shirin komawa taka leda a Sifaniya.
Magungunan gargajiya 7 da gwamnatin Najeriya ta samar domin manyan cututtuka
Har yanzu akwai miliyoyin ƴan Najeriya da ke ci gaba da amfani da magungunan gargajiya a matsayin mafita ta farko idan ba su da lafiya.
Me ya sa da wuya mu manta masoyanmu na farko?
Mutane da dama ba su taɓa mantawa da masoyansu na farko, kuma suna daga cikin abubuwan da suka fi tunawa akai-akai, amma me ya sa ake samun haka?
'Jihohin Najeriya 8 da za su fuskanci ambaliya cikin watan Agusta'
HukumarKula da harkokin ruwa ta Najeriya cikin sanarwar da ta wallafa a shafinta na X, ta lissafo wasu jihohi da take ganin suna cikin haɗarin fuskantar ambaliyar ruwa, lamarin da ka iya haddasa asarar dukiyoyi tare da tarwatsa harkokin rayuwar jama'a.
Shirye-shiryenmu
Saurari na gaba, Shirin Safe, 05:29, 2 Agusta 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Saurari, Shirin Yamma, 19:29, 1 Agusta 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban-daban na duniya.
Saurari, Shirin Hantsi, 06:30, 1 Agusta 2026, Tsawon lokaci 29,30
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Saurari, Shirin Safe, 05:29, 1 Agusta 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Wasanni
KAI TSAYE, Anya Infantino zai kai labari idan ƙuri'a za a kaɗa?
Wannan shafi ne da yake kawo muku labaran wasannin BBC Hausa na ranakun 27 ga watan Yuli, zuwa 2 ga watan Agusta 2026.
Ƙasa ɗaya a duniya da ba ta shiga harkokin kwallon ƙafa
Yayin da ƙwallon ƙafa ya kasance ɗaya daga cikin wasannin mafiya shahara a duniya, har yanzu akwai wata ƙasa da ba a damu da wasan ba.
Manyan ƙungiyoyin firimiya na bibiyar Ayyoub Bouaddi, Rulli zai bar Marseille
Ƙungiyoyin gasar firimiya uku na bibiyar ɗansan Chelsea, Liam Delap, Manchester City na zawarcin Ayyoub Bouaddi yayin da Mamadou Sangare ya kusa komawa Brentford.
Real Madrid ta nace wa Rodri, Juve ta karɓo Randal Kolo Muani
Real Madrid na da ƙwarin guiwar mallakar ɗanwasan Manchester City Rodri, Inter Milan na nace wa ɗanwasan Liverpool Curtis Jones yayin da Palmeiras ta yi watsi da tayin Aston Villa kan Allan.
Me ya sa kowace ƙasa ke son doke Najeriya?
Duk da ƙara faɗaɗa gasar, amma Najeriya ita ce tawagar da har yanzu kowa yake son ya samu nasara a kanta.
Tashar WhatsApp ta BBC Hausa
A wannan shafin za ku samu labarai daga ƙasashen Afrika da kuma sauran sassan duniya da ɗumi-ɗuminsu domin masu bibiyar mu a WhatsApp.
Kuna son tattalin datarku?
Shiga shafinmu na labarai maras hoto domin rage zuƙar data
Labarai da Rahotanni Na Musamman
Dalilai 4 da suka sa aka gaza magance matsalar tsaro a wasu jihohin Arewa
''Mun dade muna ba gwamnonin jihohin nan shawara kan abubuwan da ya kamata a yi, wadanda da an yi su da an shawo kan matsalar nan tun da dadewa.''
Ko za a iya yi wa namiji dashen mazakutarsa da aka yanke?
"Za a iya yin aiki idan an kai azzakarin cikin lokacin da ake kira da "Golden Hours" ko kuma lokutan farko. Kuma za a iya sanya azzakarin a cikin ƙanƙara bayan wankewa da naɗe shi a cikin leda.
Yadda Saudiyya ta shiga tsaka mai wuya kan yaƙin Iran da Amurka
Saudiyya na da zaɓi biyu, ko dai ta ci gaba da kai hare-hare domin kare kanta ko kuma ta ja baya domin gudun kada ta ƙara ƙazanta yaƙin.
'Biyan bashi ne ke laƙume kuɗin Najeriya da aka tara bayan janye tallafi'
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Juma'a 31 ga watan Yulin 2026.
Abubuwa 5 da suka fito game da binciken ma'aikatar bogi
A makon da ya gabata ne majalisar ta kafa kwamitin bincike, ƙarƙashin jagorancin Hon. Yusuf Gadgi, wanda ya riƙa gayyatar hukukomin gwamnati daban-daban da suka jiɓanci kafuwar ma'aikatar domin daga gare su.
Me ya sa ƴan bindiga suka fara kai wa alƙalai hari a Najeriya?
Masana harkokin tsaro na ganin hare-haren da ƴan bindiga ke kai wa alƙalai ba wai don neman kuɗin fansa kaɗai ake yi ba.
Sojojin Amurka da suka mutu da waɗanda suka jikkata a yaƙi da Iran
Aƙalla jami'an sojin Amurka 624 ne suka jikkata tun bayan da Shugaba Donald Trump ya bayar da umarnin kai hare-hare kan Iran a watan Fabrairu, bisa sabon rahoton ma'aikatar tsaro ta Pentagon da aka fitar ranar 25 ga Yuli.
Me zai faru idan Hamas ta zubar da makamanta?
Ƙungiyar Hamas da ke Gaza ta amince da "zubar da duka makamanta" sakamakon cimma yarjejeniya da kwamitin zaman lafiyar da Trump ya kafa, bayan tattaunawa ''mai zafi'' ta tsawon watanni.
'Yadda na yi auren Mutu'a na tsawon shekara biyu'
Yayin da ake ci gaba da musayar yawu dangane da halasci ko rashin halascin auren mutu'a wata wanda ta yi auren mutu'a na tsawon shekara guda ta shaida wa BBC yadda al'amarin ya faru.
Ko ficewar jiga-jigan NDC a Kano za ta karya lagon Kwankwasiyya?
A shekarar 2023 ne aka zabi Sanata Rufai Sani Hanga a matsayin ɗanmajalisar dattawan Najeriya mai wakiltar Kano ta Tsakiya a jam'iyyar NNPP Kwankwasiyya.
Me ya sa yawancin mutanen da ke tara ƙwanji ke mutuwa da wuri?
Wani bincike ya gano cewa ƙwararrun masu gina jiki da tara ƙwanji sun fi masu yin motsa jiki na nishaɗi jefi-jefi fuskantar haɗarin mutuwa ta farat-ɗaya sakamakon bugun zuciya.
Nawa ne kuɗin da Dangote ya yi alƙawarin bayarwa sadaka?
Arzikin attajirin dai ya kai dala biliyan 35.1, wanda ke nufin idan har wannan adadin ya ci gaba da kasancewa haka, kashi ɗaya bisa uku na dukiyarsa zai kai kusan dala biliyan 11.7.
KAI TSAYE - Labaran BBC Hausa
Saurari labaran BBC Hausa Kai Tsaye Litinin zuwa Juma’a da karfe 0530, 0630, 1400 da 1930 GMT, sai kuma Asabar da Lahadi da karfe 0530, 0630 da 1930 GMT.






























































